Wasanni-Faransa

PSG ta amince da sayan Mbappe kan Fam miliyan 180

Kylian Mbappe a lokacin da ya zura kwallo a ragar Borussia Dortmund, a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai da ta gabata..
Kylian Mbappe a lokacin da ya zura kwallo a ragar Borussia Dortmund, a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai da ta gabata.. Reuters/Ralph Orlowsk

Paris Saint-Germain ta amince ta biya kungiyar Monaco fam miliyan 180 domin sayan dan wasanta Kylian Mbappe.

Talla

Kungiyoyin da dukkaninsu ke buga wasan Ligue 1 na kasar Faransa, sun cimma matsayar ce a jiya Lahadi.

Cinikin dai yasa Mbappe zai zama dan wasa na biyu mafi tsada bayan Neymar, wanda shima kungiyar ta PSG ta saye daga Barcelona a kan fam miliyan 222, a farkon watan da muke ciki.

Sai dai duk da cimma yarjejeniyar Mbappe ya bayyana a bencin Monaco a wasan da suka buga a daren jiya Lahadi.

Kafafen yada labaran wasannin Faransa sun rawaito cewa yarjejeniyar farko da Mbappen zai sanya hannu ta koma kungiyar PSG ce a matsayin aro, amma daga baya kungiyar zata maida komen nasa na din-din-din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.