Wasanni-Tennis

Sharapova ta fidda Halep daga gasar US Open zagayen farko

Maria Sharapova ta kasar Rasha, yayinda take murna bayan samun nasara kan Simona Halep ta Romania a gasar kwallon Tennis ta U.S. Open a birnin New York.
Maria Sharapova ta kasar Rasha, yayinda take murna bayan samun nasara kan Simona Halep ta Romania a gasar kwallon Tennis ta U.S. Open a birnin New York. Jerry Lai-USA TODAY Sports

Maria Sharapova mai wakiltar Rasha ta taka rawar gani a agasar kwallon Tennis ta US Open da aka fara a New York, inda ta fitar da kwararriya ta biyu a wasan Tennis din a Duniya Simona Halep ‘yar Romania.

Talla

Sharapova dai ta lallasa Halep da kwallaye 6-4, 4-6, da kuma 6-3 a gaban ‘yan kallo 24,000.

Wannan dai shi ne wasan Sharapova, mai shekaru 30, a gasar Tennis ta Grand Slam karo na farko bayan kammala wa’adin watanni 15 da aka deba mata na haramcin buga wasan, sakamakon kama ta da aka yi da laifin shan kwayoyin Karin kuzari.

Masu kallo dai sun yi mamakin yadda Sharapova ta lallasa Halep tare da fitar da ita a zagayen farko na gasar, duk da cewa ita ce ta 146 a matakin kwarewa kan tennis a duniya yayinda Halep ta ke rike da matsayi na biyu.

Rabon da Sharapova ta lashe gasar ta Grand Slam dai tun a shekarar 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.