Wasanni

Olympics: Za'a mikawa 'yar Najeriya lambar Tagulla bayan shekaru 9

Maryam Usman, wadda ta wakilci Najeriya a gasar daga nauyi na kilogram 75 ajin mata, a wasannin Olympics da ya gudana a Beijing, shekara ta 2008
Maryam Usman, wadda ta wakilci Najeriya a gasar daga nauyi na kilogram 75 ajin mata, a wasannin Olympics da ya gudana a Beijing, shekara ta 2008 Punch

Kwamitin lura wasannin Olympics na Najeriya y ace a ranar Alhamis dinnan mai zuwa zai mika kyautar lambar yabo ta tagulla ga Maryam Usman, wadda ta wakilci kasar a gasar daga nauyi na kilogram 75 ajin mata, a wasannin Olympics da ya gudana a Beijing, shekara ta 2008.

Talla

Maryam zata amshe kyautar tagullan ce, sakamakon matakin da kwamitin shirya wasannin Olympics na Duniya ya dauka, na kwace kyautar lambar yabo ta azurfa da ya bai wa Koroboka Olha ta Ukraine a gasar da ta gudana a Beijing, da ta kammala a matsayi na biyu.

Kwamitin ya samu Olha ne, da lafin shan kwayoyin Karin kuzari, bayan sake gudanar da gwajin jininta da aka dauka a shekarar ta 2008.

Hakan yasa Maryam da ta kammala gasar daga nauyin a matsayi na 4, bayan da ta daga karfe mai nauyin kilogram 265, a yanzu ta koma matsayi na uku, yayinda Ele Opeloge ta Tsibirin Samoa, ta koma matsayi na 2 daga ta 3, ita kuwa Jan Mi-ran daga Korea ta Kudu tana nan a matsayinta na daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.