Wasanni

Babu ragi kan euro miliyan 200 da muka sa akan Coutinho - Liverpool

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta jaddada cewa zata saida dan wasanta Philippe Coutinho en kawai a kan kudi Euro miliyan dari biyu, farashin bisa dukkanin alamu zai tilastawa kungiyar Barcelona hadiye kawalamarta bisa dan wasan ban tana so ba.

Philippe Coutinho na kungiyar Liverpool.
Philippe Coutinho na kungiyar Liverpool. Reuters/Carl Recine
Talla

Tun a farkon watan Satumban nan Barcelona ta ce janyewar da ta yi daga burinta na sayan Coutinho daga Liverpool, a farkon bude kasuwar cinikin ‘yan wasa ta shekarar bana, ya biyo bayan tsabar farashin kudi euro miliyan 200n da Liverpool ta nema kafin sai da mata dan wasan.

To sai dai shugaban kungiyar Barcelona Josep Maria, tun da fari abinda sukai niyyar biya bisa cinikin dan wasan ba zai wuce euro miliyan 120 ba idan har yayi tsada.

Tuni dai Barcelona ta zaftare euro miliyan 105 daga euro miliyan 222 da ta samun bayan saida Neymar, inda tayi amfani da su wajen sayo Ousamne Dembele daga Burussia Dortmund, sai dai kuma a halin yanzu Dembele zai shafe watanni uku da rabi yana jiyya sakamakon raunin da ya samu a cinyarsa, yayin wasan da suka buga da Getafe, inda yayi mintuna 29 kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI