wasanni

Algeria ta ajiye zaratan 'yan wasanta a banci

Wasu daga cikin 'yan wasan Algeria
Wasu daga cikin 'yan wasan Algeria AFP PHOTO / CARL DE SOUZA

Tawagar kwallon kafa ta Algeria za ta yi wasanta da Kamaru a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba tare da zaratan ‘yan wasanta ba da suka hada da Riyad Mahrez da Nabil Bentaleb da kuma Islam Slimani.

Talla

Kasashen biyu za su fafata ne a karshen mako bayan Algeria ta sha kashi a gida da waje a karawarta da Zambia, lamarin da ya kawo cikas ga burinta na samun gurbi a gasar ta cin kofin duniya wadda za a gudanar a kasar Rasha.

Wannan ya sa Algeria a wannan karfo ta zabi amfani da sabbin ‘yan wasa a fafatawar da Kamaru, ko watakila za su yi abin azo a gani a sauran wasannin guda biyu da suka rage wa kasar.

Algeria da Kamaru da Najeriya da Zambia duk suna rukunin B kuma Najeriya ce ke jan ragama a rukunin, yayin da ake saran ta samu gurbi a gasar ta cin kofin duniya da zarar ta doke Zambia a karawar da za su yi a ranar Asabar a birnin Uyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.