wasanni

Morata na Chelsea zai yi jinyar sama da wata guda

Alvaro Morata.
Alvaro Morata. REUTERS/Giorgio Perottino

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Chelsea Alvaro Morata zai yi jinyar sama da wata guda bayan raunin da ya samu a yayin fafatawar da suka sha kashi a hannun Manchester City a ranar Asabar.

Talla

Morata mai shekaru 24 ya koma Chelsea ne daga Real Madrid akan farashin Pam miliyan 60, kuma shi ne dan wasan da ya fi ci wa Chelsea kwallaye a wannan kaka, in da ya zura kwallaye bakwai.

Kazalika dan wasan ba zai samu damar buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba da kasarsa ta Spain za ta yi da Albania da Isra’ila a wannan mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.