Wasanni

Nijar ta yi nasarar zuwa gasar neman kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17

Sauti 10:25

Karon farko a tarihi,  Nijar ta yi nasarar zuwa gasar duniya ta neman kofin kwallon kafa na matasa 'yan kasa da shekaru 17 a duniya wadda aka fara a wannan juma'a a kasar India.Abdoulaye Issa, ya yi mana dubi a game da muhimmancin wannan dama da Nijar ta sama da kuma irin kalubalen da ke gabanta lura da cewa wannan ne karon farko da ta ke halartar gasar.