wasanni

Wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya na 2018

Messi a filin wasan lokacin karawar Argentina da Peru
Messi a filin wasan lokacin karawar Argentina da Peru REUTERS/Agustin Marcarian

A yanzu dai babu tabbas idan har kasar Argentina za ta samu damar zuwa gasar neman kofin kwallon kafa na duniya da za a yi shekara mai zuwa a kasar Rasha, bayan da a cikin dare jiya kasar ta tashi canjaras a karawarta da Peru ba wanda ya zura kwallo a ragar wani duk da cewa an yi wasan ne a gidan Argentina.

Talla

Bayan wasan na jiya, a yanzu Argentina na can ne a matsayin ta 6 cikin jerin kasashen Kudancin Amurka da ke wannan yunkuri, kuma kasashe 4 na farko ne kawai ke da tabbacin shiga gasa, yayin da ya rage zagaye daya a nan gaba domin kammala fafatawa tsakanin kasashen yankin.

Idan Argentina ta gaza zuwa gasar ta neman kofin duniya a Rasha, wannan zai kasance na farko a cikin shekaru 47.

Ita ma Colombia ta sha kashi ne a karawarta da Paraguay, abin da ke nufin cewa dole ne kasar ta Colombia ta yi nasarar doke Peru a karawar da za su yi nan gaba kafin ta samu shiga wannan gasa da za a yi a kasar Rasha.

 

Wani wasan da ya bai wa masu shawarar kwallon kafa mamaki a yankin na Kudancin Amurka shi ne wanda aka yi tsakanin Uruguay da Venezuela, wasan da aka tashi ba wanda ya zura kwallo a ragar wani, to sai dai duk wannan sakamako, Uruguay na da kwarin gwiwar samun damar zuwa Rasha a badi.

 

Yankin Turai

 

Jamus ta samu gurbin shiga gasar ta neman kofin duniya, bayan da ta lallasa Ireland a karawar da suka yi cikin daren alhamis ci 3-1. Jamus dai ita ce ke rike da kofin gasar da aka buka a kasar Brazil

Wata kasar da ta yi nasarar zuwa gasar neman kofin na duniya ita ce Ingila, bayan da da kyar da jibin goshi ta doke Slovenia ci 1 mai ban haushi. Ingila ta yi nasara ne ana gaf a ta shi wannan wasa da aka buga a birnin London.

A wannan juma’a kuwa Spain ce ke shirin fafatawa da Albania, karawar da wasu ke ganin cewa abu ne mai sauki ga Spain din ta yi nasarar doke Albania.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.