wasanni

Buhari ya yaba wa Super Eagles kan nasarar zuwa Rasha

'Yan wasan Najeriya na murnar doke Zambia a birnin Uyo
'Yan wasan Najeriya na murnar doke Zambia a birnin Uyo PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga tawagar kwallon kafar kasar wato, Super Eagles  bisa nasarar samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a shekara mai zuwa bayan ta casa abokiyar karawarta, wato Zambia da ci 1-0 a birnin Uyo a ranar Asabar da ta gabata.

Talla

Shugaba Buhari ya bayyana wannan nasara a matsayin wani abu mai matukar dadi, wanda kuma ya kira shi da kyautar murnar cikar kasar shekaru 57 da samun yanci daga Turawan Birtaniya.

Shugaba ya kuma yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna goyon baya ga tawagar Super Eagles, yayin da ya bukaci hukumomin da ke kula da wasanni da su mayar da hanakali game da shirye-shiryen zuwa Rasha a badi, don ganin cewa, sun kai kasar ga gaci.

A bangare guda, wata majiya daga hukumar kwallon kafar kasar ta ce, ko wani dan wasan Super Eagles za a ba shi wani tukuici na musamman da ya kai Naira miliyan 1 saboda kokarin da suka yi a karawarsu da Zambia.

Sannan kuma wani attajiri da ake kira Cif Kensington Adebutu ya bai wa ‘yan wasan na Najeriya kyautar Naira miliyan 50 bayan kasar ta zama ta farko daga Afrika da ta samu gurbi a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.