Kwallon Kafa

Ronaldo da Messi da Neymar wa zai lashe Balon d’Or?

Neymar da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a wajen bikin bayar da kyautar gwarzon dan wasan Duniya na FIFA.
Neymar da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a wajen bikin bayar da kyautar gwarzon dan wasan Duniya na FIFA. FABRICE COFFRINI / AFP

Mujallar Faransa da ke bada kyautar Balon d’Or ta fitar da jerin ‘yan wasa 30 da suka kunshi Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Neymar Jr wadanda cikinsu daya zai lashe kyautar ta bana.

Talla

Ana sa ran Ronaldo zai lashe kyautar bayan ya taimakawa Real Madrid lashe kofin zakarun Turai a jere da jere da kuma kofin La liga a kakar da ta gabata.

Ronaldo na fatar kafa tarihin da Messi ya kafa na lashe kyautar sau biyar.

Neymar wanda ya koma PSG daga Barcelona akan kudi yuro miliyan 22, yana cikin sahun zaratan ‘yan wasan, da ke neman lashe kyautar ta Balon d’Or a bana.

Sannan baya ga Ronaldo akwai ‘yan wasan Real Madrid 7 a jerin ‘yan wasan 30 da mujallar za ta zaba gwarzon duniya da suka hada da Sergio Ramos da Karim Benzema da Isco da Marcelo da Toni Kroos da Luka Modric.

Kwallon da ta fi shahara a raga a bana

A cikin jerin ‘yan wasan 30 akwai ‘Yan wasan Afrika guda biyu Sadio Mane na Senegal da ke taka leda a Liverpool da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon da ke taka leda a Borussia Dortmund.

Ga jerin ‘yan wasan 30.

Neymar (Paris SG/BRA)

Luka Modric (Real Madrid/CRO)

Paulo Dybala (Juventus/ARG)

Marcelo (Real Madrid/BRA)

N'Golo Kante (Chelsea/FRA)

Luis Suarez (Barcelona/URU)

Sergio Ramos (Real Madrid ESP)

Jan Oblak (Atletico Madrid/SLO)

Philippe Coutinho (Liverpool/BRA)

Dries Mertens (Napoli/BEL)

Kevin De Bruyne (Manchester City/BEL)

Robert Lewandowski (Bayern Munich/POL)

David De Gea (Manchester United/ESP)

Harry Kane (Tottenham Hotspur/ENG)

Edin Dzeko (Roma/BIH)

Antoine Griezmann (Atletico Madrid/FRA)

Toni Kroos (Real Madrid/GER)

Gianluigi Buffon (Juventus/ITA)

Sadio Mane (Liverpool/SEN)

Radamel Falcao (Monaco/COL)

Lionel Messi (Barcelona/ARG)

Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund/GAB)

Edinson Cavani (Paris SG/URU)

Mats Hummels (Bayern Munich/GER)

Karim Benzema (Real Madrid/FRA)

Cristiano Ronaldo (Real Madrid/POR)

Eden Hazard (Chelsea/BEL)

Leonardo Bonucci (AC Milan/ITA)

Isco (Real Madrid/ESP)

Kylian Mbappe (Paris SG/FRA)

 

FIFA ta fitar da 'Yan wasan da suka jefa kwallo a raga mafi shahara a kakar da ta gabata.

'Yan wasan sun hada Olivier Giroud na Arsenal

Jerin kwallayen da aka ci a raga da suka shahara a bana

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.