Wasanni

Na yadda da kwarewar Harry Kane - Zidane

dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane, yayinda ya ci wa kasarsa ta Ingila kwallo a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya da suka fafata da Slovenia.
dan wasan gaba na kungiyar Tottenham Harry Kane, yayinda ya ci wa kasarsa ta Ingila kwallo a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya da suka fafata da Slovenia. REUTERS/Dylan Martinez

Yayinda a yau Talata kungiyar Real Madrid ke shirin karbar bakuncin takwararta ta Tottenham daga Ingila a cigaba da gasar zakarun kwallon kafa ta nahiyar Turai, mai horar da Madrid Zinadine Zidane, ya bayyana dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, a matsayin cikakke kuma kwararren dan wasan kwallo kafa.

Talla

Kalaman na Kocin Madrid na zuwa yayinda aka fara yankyasa cewar mai yiwuwa na gaba su nemi sayen dan wasan idan aka bude kasuwar ciniki.

Zuwa yanzu cikin wannan shekarar, Harry Kane ya ciwa Kungiyarsa ta Tottenham da ma kasarsa ta Ingila jimillar kwallaye 43 a wasanni 38 da haska.

A gefe guda kuma mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettinho, ya ce yana fatan ganin Harry Kane ya zamo madubi tamkar yadda dan wasan AS Roma Fransisco Totti ya zamewa kungiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.