Wasanni

'Yan wasan kungiyar Sunshine Stars na cikin tsaka mai wuya

Dan wasa Gedo na kungiyar Al-Ahly da ke Masar da dan wasa Tosin Yunusa na kungiyar Sunshine Stars yayin fafatawar da suka yi a gasar kungiyoyin zakarun nahiyar Afrika a birnin Cairo watan Oktoba na shekarar 2012.
Dan wasa Gedo na kungiyar Al-Ahly da ke Masar da dan wasa Tosin Yunusa na kungiyar Sunshine Stars yayin fafatawar da suka yi a gasar kungiyoyin zakarun nahiyar Afrika a birnin Cairo watan Oktoba na shekarar 2012. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Cikin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars da ke buga ajin gasar Premier ta Najeriya ya duri ruwa, bayan ya tabbata cewa hukumar gudanarwar kungiyar na shirin sallamar ‘yan wasan guda 20.

Talla

Shugabancin kungiyar yace matakin ya zama tilas domin karfafa kungiyar kafin fara sabuwar kakar wasa.

A kakar wasan da aka kammala ta Premier Najeriya, Sunshine Stars sun kare ne a matsayi na 10 da kyar da jibin goshi, abinda bai yiwa shugabancin kungiyar dadi ba.

Rahotanni daga kungiyar sun bayyana cewa tuni Kocin Kungiyar Duke Udi da tawagarsa, suka mika sunayen yan wasa 20 da ake ganin sun gaza, a kakar wasan da aka kammala.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.