Wasanni

Pogba na gab da dawowa filin wasa

Dan wasan Manchester United Paul Pogba
Dan wasan Manchester United Paul Pogba Reuters / Carl Recine Livepic

Dan wasan Manchester United Paul Pogba na gab da dawowa filin wasa, duk da dai kocin kungiyar Jose Mourinho bai ba da cikaken tabbacin yaushe Pogba zai koma taka leda ba.

Talla

United ta soma wannan kakar da karfinta, kafin rauni Pogba a karawarta da Basel a watan da ya gabata.

United ce ta biyu a teburin Frimiya, kuma ta na shirin karawar da Huddersfild Town a ranar Assabar.

Da alama Kungiyar ta yi maraicin Pogba a wasannita da suka gabata, inda ta tashi babu ci tsakanin ta da Liverpool, kazalika ta sha da kyar a hannu Benfica ci 1-0 a wasan zakarun Turai da suka fafata a Portugal ranar laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.