FIFA

FIFA: Ronaldo ne gwarzon duniya a bana

Yanzu Cristiano Ronaldo ya kamo Messi bayan lashe kyautar gwarzon duniya sau biyar
Yanzu Cristiano Ronaldo ya kamo Messi bayan lashe kyautar gwarzon duniya sau biyar Images via Reuters/John Sibley

Cristiano Ronaldo ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya na bana da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ke bayarwa duk shekara inda dan wasan na Portugal ya sake doke Messi da Neymar.

Talla

Ronaldo ya lashe kyautar ne bayan taimakawa Real Madrid kare kofin zakarun Turai da La liga.

Ronaldo ne kuma wanda ya fi cin kwallaye a gasar zakarun Turai a kakar da ta gabata da kwallo 12, inda ya kere Messi da ya ci kwallaye 11 a gasar.

Messi ne ya zo matsayi na biyu duk ya fi Ronaldo yawan kwallaye a kakar da ta gabata.

Ronaldo yanzu ya yi kafada da Messi bayan lashe kyautar sau biyar.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane kuma ya doke Antonio Conte na Chelsea da kocin Juventus Massimiliano Allegri a matsayin gwarzon koci.

Zidane ya kasance mai horar da ‘yan wasa na farko da ya kare kofin zakarun Turai.

Kungiyar FIFA XI ta kunshi ‘yan wasan Madrid 5 da suka hada da Ronaldo da Sergio Ramos da Toni Kroos da Luka Modric da Marcelo.

Sauran zaratan ‘yan wasan 11 na FIFA sun hada da Messi da Naymar da Dani Alves da Leonardo Bonucci da Andres Iniesta da Gianluigi Buffon.

Olivier Giroud ne ya lashe kyautar Puskas, kwallon da ta fi shahara a raga a kakar da ta gabata, wato kwallon da ya ci Crystal Palace kamar harbin kunama a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.