Turai

Ingila ta yi nasara kan Brazil da ci 3 da 1

Rhian Brewster ne ya zura kwallaye uku a wasan na yau daya bai wa Ingila nasarar samun damar fafatawar karshe tsakaninta da kasar da ta yi nasara a wasan gaba ranar Asabar tsakanin Mali da Italiya.
Rhian Brewster ne ya zura kwallaye uku a wasan na yau daya bai wa Ingila nasarar samun damar fafatawar karshe tsakaninta da kasar da ta yi nasara a wasan gaba ranar Asabar tsakanin Mali da Italiya. Reuters

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Liverpool Rhian Brewster ya kai kasar sa Ingila ga nasara a wasan karshe da ta kece raini da Brazil na gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 da India ke karbar bakunci.

Talla

Ingila ta lallasa Brazil da ci 3-1 a fafatawar da suka yi yau Laraba a filin wasa na Kolkata da ke India.

Brewster ne dai ya yi nasara zura dukkanin kwallayen uku a raga, inda ya zura biyu kafin hutun rabin lokaci ya kuma kara guda bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A bangare guda shi ma dan wasan Brazil Wasley ya zurawa kasar sa kwallo guda tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, kuma tun daga nan ne suka gaza tabuka abin kirki inda aka tashi a wasan uku da daya.

Brazil dai na neman mataki na 3, yayinda Ingila kuma za ta buga wasan karshe a ranar Asabar da wacce ta yi nasara tsakanin Spain ko kuma Mali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.