Wasanni

Kungiyar Leicester City ta zabi sabon mai horarwa

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Southampton Claude Puel, wanda kungiyar Leicester ta dauka a mtsayin sabon mai horar da ita.
Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Southampton Claude Puel, wanda kungiyar Leicester ta dauka a mtsayin sabon mai horar da ita. Reuters / Dylan Martinez Livepic

Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta zabi tsohon mai horar da kungiyar Southampton Claude Puel a matsayin sabon mai horar da kungiyar.

Talla

Karkashin yarjejeniyar da aka cimma Claude Puel zai shafe shekaru uku yana horar da kungiyar ta Leicester.

Puel ya taba horar da kungiyoyin Monaco, Lille, Lyon da kuma Nice, inda ya samu nasarar cin kofin gasar Faransa ta Ligue 1 tare da kungiyar Monaco a shekara ta 2000.

Sabon mai horar da Leicester ya yi takara da mai horar da kungiyar Burnley Sean Dyche, tsohon mai horar da Manchester United Manuel Pellegrini da kuma tsohon dan wasan kungiyar ta United Ryan Giggs kafin samun matsayin.

Puel shi ne mai horarwa na uku da Leicester ke dauka a jere cikin wannan shekara, kuma ya maye gurbin Craig Shakespare ne, wanda shi kuma ya karbi aikin horarwar bayan korar da Leicester ta yi wa Claudio Ranieri da ya jagoranceta lashe kofin gasar Premier ta kasar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.