Wasanni

Rashin sayen kwararren dan wasa ne ya sa aka sallame ni - Koeman

Tsohon mai horar da kungiyar Everton Ronald Koeman.
Tsohon mai horar da kungiyar Everton Ronald Koeman. Reuters/Lee Smith

Tsohon mai horar da kungiyar Everton, Ronald Koeman, ya ce gazawar kungiyar wajen sayen dan wasan gaba na Arsenal Olivier Giroud a matsayin wanda zai maye gurbin Romelu Lukaku da ya koma Manchester United, da yadda wasanni ke riskarsu a murde, sune dalilan da suka sanya aka kore shi daga aikinsa na horar da kungiyar.

Talla

A ranar Litinin da ta gabata Everton ta sallami Koeman, bayan da Arsenal ta lallasa ta da kwallaye 5-2 a gasar Premier.

Rashin nasarar ya jefa Everton ajin ‘yan dagaji dake karshen teburin tsayuwar kungiyoyin na premier.

Ba yaga Olivier Giroud na Arsenal kungiyar Everton na fatan ganin ta sayi dan wasan gaba na Chelsea Diego Cousta wanda majiya mai karfi ta ce tuni Everton din da ware masa riga.

A ranar lahadi mai zuwa Everton zata yi tattaki zuwa Leicester City karkashin sabon mai horarwa David Unsworth.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.