Isa ga babban shafi
Wasanni

Aguero ya kafa sabon tarihi a Manchester City

Dan wasan gaba na kungiyar Manchester City, Sergio Aguero yayin da yake murnar zura kwallo ta 3 a ragar kungiyar Napoli.
Dan wasan gaba na kungiyar Manchester City, Sergio Aguero yayin da yake murnar zura kwallo ta 3 a ragar kungiyar Napoli. Reuters/Andrew Boyers
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Sergio Aguero ya kafa tarihin zama dan wasan kungiyar Manchester City da yafi kowanne ci wa kungiyar kwallaye, bayanda ya zura kwallo a wasan gasar zakarun nahiyar turai da suka fafata da kungiyar Napoli, kuma suka lallasata da kwallaye 4-2.

Talla

Kwallon da Aguero ya zura a ragar Napoli a wasan na jiya, ita ce ta 178 da ya ci wa Manchester City, hakan ya bashi damar goge tarihin da dan wasan kungiyar Eric Brook ya kafa na cin kwallaye 177 a shekarar 1939.

A shekarar 1939 Brook ya ci wa City kwallo ta karshe, wanda kuma tunda daga wannan lokacin, sai da aka shafe shekaru 78 ba'a samu wanda ya goge tarihin ba, sai yanzu da Aguero ya samu nasarar hakan.

A halin yanzu daga cikin kungiyoyin da kai tsaye suka samu nasarar kai wa ga zagaye na gaba a gasar zakarun nahiyar turai, akwai, Tottenham, Manchester City, Paris Saint Germain, da kuma Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.