Wasanni

Buhari ya karrama 'yan wasan D'Tigress

'Yan wasan kwallon kwandon mata na Najeriya, D’Tigress.
'Yan wasan kwallon kwandon mata na Najeriya, D’Tigress. NAN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya cika alkawarin da ya dauka na karrama tawagar kwallon Kwando ta Najeriya ajin mata wato D’Tigress, da kyauta, bayan da suka samu nasarar lashe kofin gasar kwallon kwandon ta nahiyar Afrika, cikin wannan shekara da aka kammala a kasar Mali.

Talla

Ko wace ‘yar wasa ta samu kyautar naira Miliyan daya, yayinda masu taimakawa kungiyar wajen horarwa suka samu naira dubu dari biyar kowannensu.

A wani labarin kuma daga bangaren ajin maza, kungiyar kwallon Kwando ta Kano Pillars, ta fara gasar kwallon kwandon kalubale shiyya ta uku ta nahiyar Afrika da kafar dama, bayan da ta lallasa kungiyar Mark Mentos da ke garin Abuja da kwallaye 74-69 a wasan farko.

Kungiyoyin kwallon kwandon da ke cikin gasar shiyya ta ukun, sun hada da Gombe Bulls, Defenders of Abuja, Customs Club daga Ghana, da kuma kungiyar kwallon Kwando ta ASPAC da ke wakiltar Jamhuriyar Benin.

A ranar Asabar mai zuwa za’a karkare wannan gasa, kuma kungiyoyi guda biyu da suka fi kwazo, zasu wakilci shiyya ta ukun gasar cin kofin kalubale na kwallon kwandon nahiyar Africa da kasar Angola zata karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI