Wasanni

Magoya bayan Argentina sun fusata da Sampaoli

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya yayin da suke murnar samun nasara a kan Argentina.
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya yayin da suke murnar samun nasara a kan Argentina. Mladen ANTONOV / AFP

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Argentina Jorge Sampaoli, yana cigaba da shan suka daga ‘yan kasar, bisa yadda suka ce ya gaza faranta musu, a wasan sada zumuncin da Najeriya ta lallasa su da kwallaye 4-2.

Talla

Da farko ‘yan wasan Argentina, Sergio Aguero da Ever Banega ne suka fara jefa kwallaye buyi a ragar Najeriya yayin wasan da aka fafata shi a birnin Krasnodar na kasar Rasha.

Daga bisani ne ‘yan wasan Najeriya, Kelechi Ihenacho, Alex Iwobi da kuma Brian Idowu suka jefa kwallaye 4 da suka bai wa najeriya nasarar kan Argentina.

A ranar Talata da aka buga wasan sada zumuncin ne kuma aka garzaya da dan wasan gaba na Argentina kuma dan kungiyar Manchester City Sergio Aguero asibiti bayan suman da yayi a dakin canza kaya, a lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci.

Sai dai daga baya jami’an lafiya sun ce ba rashin lafiya mai tsauri ce ta samu dan wasan ba, kuma har ya murmure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.