Wasanni

An samu karin 'yan wasan Italiya da zasu daina wasa

Wasu daga cikin 'yan wasan kasar Italy da suka hada da Gianluigi Buffon, da kuma Andrea Barzagli, bayan wasan da suka tashi 0-0 tsakaninsu da Sweden November 13, 2017.
Wasu daga cikin 'yan wasan kasar Italy da suka hada da Gianluigi Buffon, da kuma Andrea Barzagli, bayan wasan da suka tashi 0-0 tsakaninsu da Sweden November 13, 2017. REUTERS/Max Rossi

Wasu Karin ‘yan wasan Italiya da suka hada da Daniele De Rossi, Giorgio Chiellini and Andrea Barzagli sun ce zasu yi ritaya daga bugawa kasar ta su wasa, bayan da suka gaza samun nasarar cancantar zuwa gasar cin kofin duniya da za’a yi Rasha.

Talla

Bayan wasan da suka buga a tsakaninsu da Sweden inda aka tashi canjarasa, 0-0 a ranar Litinin mai tsaron Raga Gianligui Buffon ya sanar da kawo karshen wasansa a matakin kasa, baya da ya buga mata wasanni 175.

Shi kuwa De Rossi, mai shekaru 34, ya ci wa Italiya kwallaye 21 ne a wasanni 117 da ya fafata, wanda a yanzu ya zarta Andrea Pirlo zama dan wasa na hudu a tarihin kwallon kafar Italiya, da ya fi buga mata yawan wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.