Ronaldo na Real Madrid ya sake kafa tarihi

Christiano Ronaldo na Real Madrid
Christiano Ronaldo na Real Madrid REUTERS/Sergio Perez

Gwarzon dan wasan duniya Christiano Ronaldo ya sake kafa tarihi a gasar zakarun nahiyar Turai, in da kawo yanzu ya zura kwallaye 18 a gasar ta bana.

Talla

Dan wasan ya zura kwallaye biyu a fafatawar da suka yi a jiya da Apoel Nicosia, abin da ya kara yawan kwallayen da ya ci a bana.

Nasarar da Madrid ta samu akan Apoel Nicosia da jumullar kwallaye 6-0 ta bai wa kungiyar damar tsallakawa zuwa matakin gaba a gasar, wato makin kungioyoyi 16 da  za su saura a gasar.

Madrid a karkashin kocinta Zinedine Zidane, ta lashe kofin zakarun Turai har sau biyu a jere amma Barceolna ta ba ta tazarar maki 10 a gasar La Liga ta Spain.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.