Duniya

Babu yadda za ayi mu zama abokai da Ronaldo -Messi

Messi ya yi imanin cewa akwai zaratan 'yan wasa masu jini a jika da ke tasowa yanzu haka wadanda kuma dole ne su kwace kambun da suke takama da shi a yanzu.
Messi ya yi imanin cewa akwai zaratan 'yan wasa masu jini a jika da ke tasowa yanzu haka wadanda kuma dole ne su kwace kambun da suke takama da shi a yanzu. Fuente: Reuters/Henry Romero

Dan wasan kwallon kafa na kungiyar Barcelona Lionel Messi ya ce ba zai taba yiwuwa su iya zama abokanai na kut da kut da zakaran kwallon kafa na Duniya Cristiano Ronaldo ba.

Talla

A cewar Messi ba wai rashin jituwa ne ko kuma tsanar juna tsakaninsa da Ronaldo ba, amma basu fahimci junansu kamar yadda ya kamata ba, hasalima basa samun damar ganawa ko tattaunawa da juna sai a wuraren bikin bada lambar yabo.

‘Yan wasan biyu dai na kungiyar Barcelona da Real Madrid na tafiya kusan kafada-kafada da juna musamman a bangaren gasar Laliga da kuma kyautukan girmamawa.

Dukkanin ‘yan wasan biyu dan Portugal da dan Argentina wadanda kuma suke taka leda a kungiyoyin kwallon kafar Spain yanzu haka sun haura shekaru 30 a duniya, inda Messi ya yi imanin cewa lokaci ya kusa da yara ‘yan kwallo masu tasowa za su karbe matsayinsu, yana mai cewa akwai ‘yan wasa da dama da yanzu haka za su iya karbe kambun zakaran kwallon kafar da duniya da suka kunshi Neymar da Mbappe da kuma Luis Suarez.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.