wasanni

Kofin firimiya:Conte ya hakikance kan maganarsa

Antonio Conte
Antonio Conte Reuters/Alessandro Garofalo

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Antonio Conte ya hakikance kan maganarsa ta cewa, mawuyaci ne Chelsea ta kare kanbita a wannan kakar ta gasar firimiya a Ingila.

Talla

A ranar Asabar da ta gabata ne, Conte ya bayyana cewa, kokarinsu na kare kanbin ya kawo karshe bayan West Ham da doke su da ci 1-0.

Sai da a jiya Talata Chelsea ta farfado bayan ta lallasa Huddersfiled da ci 3-1, yayin da Conte ya gargadi ‘yan wasansa cewa, har yanzu akwai tazarar maki 11 tsakaninsu da Manchester City mai jan raga a teburin gasar.

A cewar Conte, kungiya kamar Manchester City wadda ke lashe kusan dukkanin wasanninta a bana, babbar barazana ce, kuma idan aka yi la’akari da haka, mawuyaci ne Chelsea ta yi tunanin za ta kare kofin da ta lashe a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI