Fam miliyan 300 da muka batar wajen sayen ‘yan wasa bai isa ba - Mourinho

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. Reuters/Robert Pratta

Mai horar da Manchester United Jose Mourinho, ya ce fan miliyan miliyan 300 da ya kashe wajen sayen ‘yan wasa a kokarin farfado da karfin kungiyar ba zai kammala biyan bukatar burin da yake son cimma ba.

Talla

Mourinho ya bayyana haka ne jim kadan bayan wasan Premier da kungiyarsa ta tashi 2-2 tsakaninta da Burnley a ranar Talatar nan.

a watan Mayu na shekarar 2016 da ta gabata Mourinho ya fara aikin horar da United, inda ya kafa tarihin sayan dan wasan tsakiya Paul Pogba daga Juventus kan fam miliyan 89, dan weasa mafi tsada a waccan lokacin.

A dai shekarar ta 2016 Mourinho ya sayo dan wasan baya Eric Bailly kan Fam miliyan 30 da kuma dan wasan tsakiya Henrikh Mkhitaryan kan fam miliyan 26.3

A wannan shekara ta 2017 da ke karewa kuwa United ta sayi Romelu Lukaku dan wasan gaba daga Everton kan fam miliyan 75, dan wasan baya Victor Lindelf kan fam miliyan 31, da kuma dan wasan tsakiya Nemanja Matic kan fam miliyan 40.

Mourinho ya koka bisa cewar United ta maida hankali ne wajen sayo ‘yan wasan baya a maimakon masu jefa kwallaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI