Wasanni

Philippe Coutinho ba na sayarwa bane - Klopp

Dan wasan kungiyar Liverpool Philipp Coutinho
Dan wasan kungiyar Liverpool Philipp Coutinho Reuters/Carl Recine

Mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya jaddada cewa dan wasansa Philippe Coutinho ba na sayarwa bane, dan haka babu wata magana a kasa, dangane da yiwuwar sauya shekar dan wasan zuwa kungiyar Barcelona cikin wannan wata na Janairu.

Talla

Kalaman na Klopp sun zo kwanaki kalilan, bayanda kamfanin Nike mai sana’anta kayayyaki daban daban da suka hada da na kwallon kafa, wanda kuma ke yi wa Barcelona riga, ya yi tallar rigar kungiyar da sunan Coutinho a kai, wanda kuma ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a karshen makon da ya gabata.

Coutinho dai bai samu damar buga wasan da Liverpool ta samu nasara kan Burnley da kwallaye 2-1 ba, sakamakon raunin da yake fama da shi a cinya, kamar yadda mai horarwa Klopp ya tabbatar, sabanin alakanta rashin bayyanar Coutinho da wasu ke yi da shirin komawarsa Barcelona.

A shekarar bara Barcelona ta yi kokarin gamsar da Liverpool don sayar mata ta Coutinho kan euro miliyan 100, yunkurin da bai nasara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.