Wasanni

Da mun yi rashin nasara akan Chelsea zan kashe kaina - Wenger

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger. Reuters/Matthew Childs

Mai horar da kungiyar Arsenal, Arsene Wenger, ya ce da dan wasansa Hector Bellerin bai rama musu kwallo ta biyu da kungiyar Chelsea ta jefa musu ba, da ya kashe kansa.

Talla

Wenger ya bayyana haka ne bayan kammala wasan Premier na jiya, tsakanin Arsenal da Chelsea inda aka tashi 2-2.

Kafin buga wasan, Arsene Wenger ya caccaki alkalan wasannin da ke busa a gasar Premier da cewa rashin kwarewarsu tasa suna aiki tamkar wadanda har yanzu kwakwalwarsu suke shekarun 1950.

Zalika Wenger ya zargi jami’an da ke shirya wasannin na Premier, da nunawa Arsenal rashin adalci, tare da hadin bakin tabbatar da cewa a mafi akasarin lokuta ana samun nasara akan kungiyar tasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.