Wasanni

CAF za ta zabi gwarzon dan wasan nahiyar Afrika

Aubameyang, Sadio Mane, da kuma Mohammed Salah dake takara kan kyautar gwarzon dan wasan nahiyar Afrika.
Aubameyang, Sadio Mane, da kuma Mohammed Salah dake takara kan kyautar gwarzon dan wasan nahiyar Afrika. Daily Guide Africa

A Yau Alhamis, a birnin Accra da ke Ghana, hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF, za ta zabi gwarzon dan wasan kwallon kafar nahiyar Afrika na shekarar 2017.

Talla

‘Yan wasa uku da hukumar zata tantance sune Muhd Salah na Masar da ke kungiyar Liverpool, sai Sadio Mane dan Senegal, shi ma dai da ke bugawa kungiyar ta Liverpool.

Dan wasa na uku shi ne, Pierre-Emerick Aubameyang dan kasar Gabon da ke bugawa kungiyar Borussia Dortmund.

Daga shekarar 2011, zuwa ta 2014, Yaya Toure, dan kasar Cote d'Ivoire ne ya rika lashe wannan kyauta, sai a 2015 da Pierre-Emeric Aubameyang na kasar Gabon ya karbe ta.

A shekarar 2016 kuma Riyad Maharez dan kasar Algeria, da ke yi wa kungiyar Leicester City wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.