Wasanni

Arsenal na fatan maye gurbin Sanchez da Aubameyang

Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez da Pierre-Emerick Aubameyang na kungiyar Borussia Dortmund.
Dan wasan Arsenal Alexis Sanchez da Pierre-Emerick Aubameyang na kungiyar Borussia Dortmund. YouTube

Majiyoyi kwarara, ciki har da kafar yada labaran wasanni ta Skysports, sun rawaito cewa Pierre-Emeric Aubameyang na kungiyar Borussia Dortmund, shi ne dan wasa na farko da Arsenal zata nemi saye, domin maye gurbin Alexis Sanchez.

Talla

Zabin sayo Aubameyang yana da nasaba da yadda tauraruwar dan wasan ke haskawa, kasancewar kwallaye 13 ya samu nasarar ci wa kungiyarsa ta Dortmund, daga cikin wasannin Bundesliga 15 da ya buga mata.

Shirye-shiryen na kungiyar Arsenal, ya biyo bayan kyautata zaton cewa ko wane lokaci Sanchez zai iya amsa tayin kungiyar Manchester City.

A watan Agustan shekarar 2017, City ta yi yunkurin sayan Sanchez daga Arsenal, inda ta yi tayin biyan euro miliyan 60 kan dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.