Damben zamani

Francis Ngannou zai karawa da Ba’amaruke Stipe Miocic

Francis Ngannou, dan Damben kasar Kamaru
Francis Ngannou, dan Damben kasar Kamaru Gregory Shamus / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Ranar 20 ga watan janairu shekarar bana ne dan wasan damben zamani na kasar Kamaru Francis Ngannou zai karawa da Ba’amaruke Stipe Miocic a mataki na zaman zakaran Damben Duniya bangaren masu nauyi Ultimate Fighting Championship UFC.Za a yi wannan karawa ne ranar 20 ga wannan watan da muke cikin sa a birnin Boston na kasar Amurka.

Talla

Dan kasar ta Kamaru Francis Ngannou na samu goyan bayan da ya dace daga ma’abuta damben zamani duk da yake bai kai matsayin Conor Mc Gregor wanda ya sha’ara a bangaren Damben zamani a Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.