wasanni

Wenger ya kira alkalin wasa da "mara gaskiya"

Arsene Wenger na Arsenal
Arsene Wenger na Arsenal Reuters/Michael Dalder

Hukumar kwallon kafar Ingila ta ce, kocin Arsenal Arsene Wenger ya kira alkalin wasa Mike Dean da "mara gaskiya" kuma "mai abin kunya" bayan Arsenal ta tashi wasa 1-1 da West Brom a jajibirin ranar bikin Kirismati.

Talla

A na dad da tashi wasan ne, alkalin ya bai wa West Brom damar bugun daga kai sai mai tsaren gida, abin da ya bai wa West Brom damar barke kwallon da Arsenal ta jefa ma ta.

Wenger ya bi alkalin har cikin dakin kintsawar jami’an kwallon kafa, in da cikin kakkausar murya ya tinkare shi kamar yadda kwamitin ladabtarwa mai zaman kansa na hukumar ya ce.

Alakalin ya ce, Wenger ya fada ma sa cewa, ya sha yanke wa Arsenal irin wannan hukunci.

A ranar 5 ga watan Janairu, kwatin ladabtarwar  ya haramta wa Wenger tsayawa dab da filin wasa a wasanni uku tare da cin tarar sa Euro dubu 40 saboda wannan laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.