Ronaldo ya bukaci Madrid ta gaggauta sayen Neymar
Wallafawa ranar:
Tsohon dan wasan gaba na Kungiyar Real Madrid dan kasar Brazil Ronaldo de Lima, ya shawarci tsohuwar kungiyar tasa ta Madrid da ta gaggauta saye tsohon dan wasan Barcelona da a yanzu ya ke PSG Neymar da Silva Santos.
A cewar Ronaldo, Madrid kungiya ce da ke bukatar kwararrun ‘yan wasa a koda yaushe, wanda kuma Neymar ke cikinsu.
A shekarar da ta gabata ne Neymar ya sauya sheka zuwa kungiyar PSG daga Barcelona kan euro miliyan 222, wanda ya sa shi zama dan wasa mafi tsada a duniya.
Sai dai duk da rahotannin da ke zagaya kafafen yada labarai kan cewa Neymar yana gaf da sauya sheka zuwa Madrid, Ronaldo de Lima ya musanta masaniyar tabbatuwar hakan.
A wani labarin kuma Ronaldo de Lima, ya ce Real Madrid zata iya sake lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai karo na uku a jere, duk da tarin kalubalen da kungiyar ke fuskanta a kakar wasa ta bana, inda ta ke matsayi na 4 a teburin La liga, da kuma tazarar maki 19 tsakaninta da abokiyar hamayyarta Barcelona da ke matsayi na daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu