Wasanni

Gasar Zakarun Turai: Liverpool ta lallasa FC Porto a Portugal

Dan wasan Liverpool Sadio Mane yayin murnar zura kwallo ta farko a ragar kungiyar FC Porto.
Dan wasan Liverpool Sadio Mane yayin murnar zura kwallo ta farko a ragar kungiyar FC Porto. Reuters/Matthew Childs

Kungiyar Liverpool ta yi tattaki har kasar Portugal inda ta lallasa kungiyar FC Porto da kwallaye 5-0.

Talla

Karo na farko kenan cikin shekaru tara da Liverpool ta buga wasan zakarun nahiyar turan a matakin gaba da na rukuni, wato na kungiyoyi 16, bayan wasan da ta buga a shekarar 2009, tsakaninta da Chelsea in da ta yi rashin nasara da 7-5 a dukkanin wasannin da suka buga a matakin gaf da kusa da na karshe.

Dan wasan Liverpool Sadio Mane dan kasar Senegal, ya kafa tarihin zama dan wasan kungiyar da ya ci mata kwallaye uku a wasa guda, yayin da suka yi tattaki zuwa gidan wasu, tun bayan bajintar da tsohon dan Liverpool Micheal Owen ya yi a shekarar 2002.

Sauran 'yan wasan Liverpool da suka zurwa kwallaye a ragar FC Porto sun hada da
Mohamed Salah da kuma Roberto Firmino Barbosa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI