UEFA zata zabi gwarzon dan wasa a gasar zakarun turai
Wallafawa ranar:
Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA, ta zabi dan wasan gaba na kungiyar Liverpool kuma dan kasar Senegal, Sadio Mane cikin ‘yan wasan za’a zabi daya tilo don karrama shi da kyautar, gwarzon dan wasan gasar zakarun turai na mako.
Tauraruwar Mane ta kara dagawa ne, bayan da ya jefa kwallaye 3 a ragar kungiyar FC Porto da suka lallasa ta ta kwallaye 5-0, bayan tattakin da suka yi har can kasar Portugal.
Zuwa yanzu dai ‘yan wasa guda hudu hukumar UEFA ta ware, wadanda daga ciki zata tantance gwarzon dan wasan gasar zakarun turan na mako.
‘yan wasan sun hada da Ilkay Gundogan na kungiyar Manchester City, Christian Eriksen na kungiyar Tottenham, Marcelo na kungiyar Real Madrid da kuma Sadio Mane na kungiyar Liverpool.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu