Wasanni

Wasanmu da PSG a Faransa ba mai sauki bane - Zidane

Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane.
Mai horar da kungiyar Real Madrid Zinedin Zidane. Reuters/Juan Medina

Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya ce ‘yan wasansa zasu iya shan wahala sosai a zagaye na biyu na wasan da zasu yi tattaki zuwa Faransa don karawa da kungiyar PSG, a gasar zakarun turai mataki na kungiyoyi 16.

Talla

A zagayen farko na wasan dai Real Madrid ta lallasa PSG da kwallaye 3-1, wadanda Critiano Ronaldo da Marcelo suka ci, yayin da suka karbi bakuncin PSG din a filin wasa na Satiago Bernabeu.

Zidane dai ya yi gargadin cewa dole Real Madrid ta jajirce a wasa na biyu da zata yi tattaki zuwa Faransa, ba tare da la’akari da nasarar farko da suka samu kan kungiyar ba.

Tun a farkon kakar wasa ta bana Real Madrid ke fuskantar kalubalen koma baya kan nasarorin da ta saba samu a wasanninta, musamman na gida Spain wato La Liga.

Kalaman na Zidane sun zo ne a dai dai lokacin da shi ma, dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, ya jadadda cewa kungiyar tasa, zata iya kai wa ga zagaye na gaba a gasar zakarun turan, duk kuwa da rashin nasarar da suka yi a hannun Real Madrid a Spain, ranar Laraba da ta gabata.

Ko da yake Neymar ya ce wasan zagaye na biyu da zasu fafata a ranar 6 ga watan Maris mai wahala ne, yana da kwarin gwiwar zasu iya samun nasara akan yaran Zidane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI