Wasanni

Gasar Olympics: Rasha ta biya tarar dala miliyan 15

Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha 28, da aka dagewa haramcin shiga wasani har abada, tare da Shugaban kasarsu Vladmir Putin.
Wasu daga cikin 'yan wasan motsa jiki na Rasha 28, da aka dagewa haramcin shiga wasani har abada, tare da Shugaban kasarsu Vladmir Putin. Reuters

Rasha ta biya tarar dala miliyan 15 da kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC, ya yanka mata a watan Disambar bara.

Talla

Biyan tarar na daga cikin sharuddan da kwamitin na IOC ya gindaya domin nazari kan yiwuwar dage haramcin shiga gasar Olympics da ya kakabawa Rasha kafin Rufe gasar ta hunturu da ke gudana a Pyeongchang a Korea ta Kudu ranar Lahadi.

A ranar 5 ga watan Disambar bara kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya IOC ya tabbatar haramta wa baki dayan ‘yan wasan Rasha shiga wasannin Olympics da za'a yi a kasar Korea ta Kudu, bayan samun tabbacin cewa, gwamnatin kasar ta goyi bayan ‘ya wasanta na motsa jiki, da su sha kwayoyin Karin Kuzari a gasar Olympics din da suka karbi bakunci cikin shekarar 2014 a birnin Sochi.

Sai dai daga bisani dai kwamitin ya kyale wasu ‘yan wasan kasar ta Rasha 168 da su shiga gasar Olympics ta hunturu, da ke gudana a Korea ta Kudu amma ba a matsayin suna wakiltar kasar su kai tsaye ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI