Wasanni

Lewandowski na gaf da cimma yarjejeniya da Real Madrid

Robert Lewandowski na Bayern Munich yayin murnar jefa kwallo ta hudu a ragar kungiyar Besiktas a gasar Zakarun Nahiyar Turai. 20 ga Fabarairu, 2018.
Robert Lewandowski na Bayern Munich yayin murnar jefa kwallo ta hudu a ragar kungiyar Besiktas a gasar Zakarun Nahiyar Turai. 20 ga Fabarairu, 2018. REUTERS/Michaela Rehle

Dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandowski, ya ki sa hannu kan tayin sabuwar yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar, a dai dai lokacin da ta tabbata cewa dan wasan yana shirin sauya sheka ne zuwa Real Madrid.

Talla

Tuni dai aka tattaunawa tsakanin Lewandoski da Real Madrid, domin tabbatar da sauyin shekar tasa a karshen kakar wasa ta bana.

Ana hasashen cewa Madrid ta karkata zuwa sayen Lewandoski ne, bisa fargabar ba lallai bane sauyen shekar dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane zuwa gareta ta ya tabbata a nan kusa.

Lewondoski ya bugawa Bayern Munich wasanni 193 inda ya jefa kwallaye 148.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI