Isa ga babban shafi
Wasanni

"Neymar ba zai iya maida PSG babbar kungiya ba"

Tsohon mai horar da kungiyar AC milan Arrigo Sacchi.
Tsohon mai horar da kungiyar AC milan Arrigo Sacchi. REUTERS/Jorge Adorno
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta AC Milan Arigo Sacchi, ya ce sayan Neymar da PSG ta yi, bai isa bai wa kungiyar damar yin kafada da kafada da sauran manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya ba.

Talla

Sacchi wanda ya jagoranci kungiyar AC Milan wajen lashe kofunan gasar zakarun turai biyu a jere cikin shekarun 1989 da 1990, ya ce bai gamsu da irin salo ko matakan da kungiyar PSG ke dauka ba domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, a kokarin da ta ken a yin fice a fagen kwallon kafa.

Idan za’a iya tuna wa PSG ta kashe kudi euro miliyan 400 wajen sayen dan wasan gaba na kungiyar Barcelona neymar akan euro miliyan 222 mafi tsada a duniya, da kuma matashin dan wasan gaba na kungiyar Monaco Kylian Mbappe akan euro miliyan 180, bayaga sauran cinikayyar ‘yan wasan da ta yi.

Sai dai duk da haka ta gaza kai wa matakin gaf da kusa da karshe a gasar zakarun turai, fafutukar da ta ke yi tun daga shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.