Isa ga babban shafi
Wasanni

"Neymar zai iya shafe watanni 5 yana jiyya"

Dan wasan PSG Neymar a lokacin da ya samu rauni a kafa cikin watan Fabarairu.
Dan wasan PSG Neymar a lokacin da ya samu rauni a kafa cikin watan Fabarairu. REUTERS/Stephane Mahe
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Wani kwararren likita a kudancin Amurka Carlinhos Vidente, ya yi hasashen Neymar ba zai samu damar bugawa kasarsa Brazil wasannin da zata yin a cin kofin duniya a Rasha ba.

Talla

Vidente, ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gargadin cewa Neymar zai shafe tsawon watanni 5 zuwa 7 yana jiyyar raunin da ya samu a kafa, muddin ana bukatar ya warke sarai.

Neymar ya samu raunin ne a wasan da suka lallasa kungiyar Marseille da kwallaye 3-0 a watan Fabarairu da ya gabata, kuma da farko an yi zaton gurdewa ya yi a kafa.

Daga bisani ne likitoci suka gano cewa ya samu tsagewar kashin kafarsa da ke hade da ‘yan yatsu 'Metatarsals' a turance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.