wasanni

Barcelona da Real Madrid na zawarcin Salah na Liverpool

Dan wasan Liverpool  Mohamed Salah ya zura kwallaye 28 a kakar bana a gasar firimiyar Ingila
Dan wasan Liverpool Mohamed Salah ya zura kwallaye 28 a kakar bana a gasar firimiyar Ingila Reuters/Lee Smith

Wasu rahotanni daga Birtaniya na cewa, manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Barcelona da PSG da kuma Real Madrid, na sha'awar kulla kwantiragi da dan wasan gaba na Liverpool wato, Mohamed Salah.

Talla

Rahotannin na cewa, manyan kungiyoyin sun shirya ajiye zunzurutun fam miliyan 200 a matsayin farashin Salah mai shekaeru 25 kuma dan asalin kasar Masar.

Tauraron dan wasan na Masar na matukar haskawa a ‘yan kwanakin nan, in da ya zura kwallaye 28 a kakar gasar firimiyar Ingila ta bana.

Sai dai ana ganin mawuyaci ne Liverpool ta sallama dan wasan ga wata kungiya, lura da cewa tana hararar lashe kofin firmiyar Ingila a kaka mai zuwa, kuma rashin Salah ka iya zama barazana a gare ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.