Wasanni

Salah ba zai koma Barcelona da Real Madrid ba

Mohamed Salah a yayin murnar zura kwallaye hudu a wasan da Liverpool ta doke Watford da ci 5-0 a ranar Asabar
Mohamed Salah a yayin murnar zura kwallaye hudu a wasan da Liverpool ta doke Watford da ci 5-0 a ranar Asabar REUTERS/Phil Noble

Wata majiya mai tushe ta shaida wa kafar ESPN cewa, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ba za ta siyar da Mohamed Salah ba a wannan kaka ga wata kungiya.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni na cewa, manyan kungiyoyin Turai da suka hada da Barcelona da Real Madrid da PSG sun nuna sha’awaru ta siyan dan wasan mai shekaru 25.

Dan wasan dai ya zura kwallaye 36 a cikin wannan kaka, sannan kuma ya ci wa Liverpool kwallaye hudu a wasan da ta casa Watford da ci 5-0 a ranar Asabar.

A yayin zantawa da shi, Salah ya shaida wa kafar ESPN cewa, yana cikin farin ciki a kungiyar ta Liverpool kuma yana burin taimaka ma ta lashe kofin firimiyar Ingila a kaka mai zuwa.

Salah ya kuma kafa tarihin kasancewa dan wasan da ya fi zura kwallaye a Anfiled a cikin kaka guda, in da ya zarce Fernendo Torres mai kwallaye 33.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.