Wasanni

Gasar zakarun turai: Klopp ya jinjinawa bajintar 'yan wasansa

Dan wasan kungiyar Liverpool Mohammed Salah yayin murnar zura kwallo a ragar kungiyar Roma, yayin zagayen farko na gasar zakarun nahiyar turai, wasan kusa da na karshe.
Dan wasan kungiyar Liverpool Mohammed Salah yayin murnar zura kwallo a ragar kungiyar Roma, yayin zagayen farko na gasar zakarun nahiyar turai, wasan kusa da na karshe. Phil Noble/Reuters

Mai horar da kungiyar Liverpool Jurgen Klopp, ya jinjinawa ‘yan wasansa bisa bajintar da suka nuna, a wasan kusa da na karshe na gasar zakarun turai, inda suka lallasa kungiyar Roma da kwalaye 5-2.

Talla

Klopp ya ce ko da yake yana kwarin gwiwar kungiyar tasa zata samu nasara akan Roma, bai yi tsammanin nasarar zata kai girman haka ba, musamman idan akai la’akari da irin bajintar da ‘yan wasan na Roma suka nuna wajen fitar da kungiyar Barcelona daga gasar.

Muhammad Salah da Roberto Firmino ne suka ci wa Liverpool kwallye biyu kowannensu, yayin da Sadio Mane ya ci wa kungiyar ta su kwallo guda.

Sai dai kaftin din kungiyar ta Liverpool Jordan Henderson ya yi gargadin dole su yi taka tsantsan a wasa na gaba da zasu yi tattaki zuwa Italiya domin sake fafatawa da Roma, gudun kada abinda ya faru ga Barcelona ya auku akansu.

A waccan lokacin, yayin wasan gaf da na kusa da na karshe, Barcelona ta Lallasa Roma da kwallaye 4-1 a Spain, amma da a wasan zagaye na biyu da Roma ta karbi bakuncin Barcelona labari ya canza, inda Romar ta lallasata da kwallaye 3-0, abinda ya bata dama fitar da Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI