Wasanni

Real Madrid ta lallasa Bayern Munich a Allianz Arena

'Yan wasan Real Madrid a lokacin da suke murnar kwallon da Marcelo ya zura a ragar Bayern Munich.
'Yan wasan Real Madrid a lokacin da suke murnar kwallon da Marcelo ya zura a ragar Bayern Munich. Kai Pfaffenbach/Reuters

Real Madrid ta kara matsawa gaf da burinta na kai wa ga zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun turai, bayan da ta yi tattaki zuwa Jamus, inda ta samu nasara akan Bayern Munich da kwallaye 2-1, a wasan kusa dana karshe.

Talla

Da fari dan wasan Munich Joshua Kimmich ne ya zura kwallo a ragar Madrid, daga bisani Marcelo ya rama mata, sai kuma Marco Asensio da ya ci wa Madrid din kwallo ta 2.

A ranar Talata mai zuwa Real Madrid zata karbi bakuncin Bayern Munich a Spain.

Kafin wasan na jiya dai mai horar da Madrid Zinaden Zidane ya sha alwashin ‘yan wasansa zasu bada himma wajen neman nasara da akalla kashi 150 bisa dari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.