wasanni

Kasa guda ce ya kamata da karbi bakwancin gasar duniya-Blatter

Sepp Blatter, tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya
Sepp Blatter, tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya REUTERS/Pierre Albouy

Tsohon shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, Sepp Blatter ya jaddada ra’ayinsa na ganin an bai wa kasa guda izinin karbar bakwancin gasar cin kofin duniya a maimakon kasashe da dama su yi tarayya wajen daukan nauyin gasar.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan kasashen Amurka da Canada da Mexico sun bayyana shirinsu na neman izinin daukan nauyin gasar a shekarar 2026, in da ma masu shirya gasar a wadannan kasashe suka ce, FIFA za ta samu ribar kudaden da yawansu ya kai Dala biliyan 11 daga karbar bakwancin na hadin gwiwar.

Tuni ita ma kasar Maoroco ta bayyana shirinta na karbar bakwancin gasar, in da kuma ta samu gagarumin goyon baya a ‘yan makwannin da suka gabgata.

Morocco ta gabatar wa hukumar FIFA wani littafi mai shafuka 193, in da ta zayyana dalilanta filla-filla na son daukar nauyin wanann gasa a 2026.

Koda yake a ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa ne za a kada kuri’ar bai wa kasar da za ta karbai bakwancin gasar izini.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.