Isa ga babban shafi
wasanni

Chelsea ta gamu da cikas na samun gurbi a gasar zakarun Turai

Kocin Chelsea,  Antonio Conte
Kocin Chelsea, Antonio Conte REUTERS
Minti 2

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce, kungiyar  ce ke da laifi bayan fafutukarta ta neman gurbi a gasar zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa ta gamu da cikas sakamakon kunnen doki da ta yi da Huddersfield 1-1 a wasan da suka kara a jiya a gasar firimiyar Ingila a Stamford Bridge.

Talla

'Yan wasan Huddersfield sun yi kokarin samun makin da suke bukata don matsawa saman teburin gasar, yayin da suka yi ta nuna maurna tare da magoya bayansu bayan busar karshe.

Duk da cewa Chelsea ta mamaye rike kwallo a wasan na jiya, amma ta gaza zura kwallaye a ragar Huddersfiled.

Chelsea ta kai hare-haren kwallaye masu kyau har sau biyar amma dukkaninsu sun bare, yayin da yanzu take matsayi na biyar akan teburin gasar ta firimiyar Ingila duk kuwa da fafutukar ta ganin ta kammala kakar wasannin da akalla a matsayi na hudu a teburin.

Ko da yake akwai wasa guda da ya rage wa Chelsea din a ranar Lahadi mai zuwa, in da za ta kara da Newcastle.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.