Isa ga babban shafi
Wasanni

Salah ya bayyana tsaffin 'yan wasa uku da suka fi burge shi

Dan wasan kungiyar Liverpool Mohamed Salah.
Dan wasan kungiyar Liverpool Mohamed Salah. Reuters/Lee Smith
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Mohamed Salah, na kungiyar Liverpool ya bayyana shahararrun ‘yan wasan da suke matukar burge shi, yake kaunarsu tare da fatan yin koyi da su.

Talla

Salah mai shekaru 25, ya ce tun yana karami, yake matukar kaunar kallon wasannin Zinaden Zidane mai horar da Real Madrid a yanzu, Ronaldo Nazario na Brazil, da kuma Francesco Totti na Italiya, kuma tsohon dan wasan AS Roma.

A cewar Mohamed Salah, ya ji dadin sa’ar da ya samu ta buga wasanni tare da Francesco Totti a kungiyar Roma kafin dan wasan ya yi ritaya daga kwallon kafa.

A ranar Alhamis da ta gabata akai bikin karrama Mohamed Salah a matsayin dan wasan Liverpool mafi kwazo a kakar wasa ta bana.

Dan wasan ya samu nasarar ci wa kungiyarsa ta Liverpool kwallaye 43 a dukkanin wasannin da ya buga mata a wannan kakar wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.