Isa ga babban shafi
Wasanni

Neymar ya koma Atisaye gadan-gadan

Neymar Junior dai na cikin tawagar 'yan kwallon da za su wakilci Brazil a gasar cin kofin duniya ta bana da za ta gudana a Rasha duk da cewa kawo yanzu bai kammala murmurewa ba.
Neymar Junior dai na cikin tawagar 'yan kwallon da za su wakilci Brazil a gasar cin kofin duniya ta bana da za ta gudana a Rasha duk da cewa kawo yanzu bai kammala murmurewa ba. REUTERS/Benoit Tessier
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Dan wasan Brazil da ke taka leda a PSG ta Faransa Neymar Junior ya koma atisaye ka’in da na’in bayan shafe kusan watanni uku yana jinya sakamakon karayar da ya samu a kafarsa.

Talla

Neymar dan wasa mafi tsada a duniya, rabon shi da filin kwallo tun karshen watan Fabarairu, ko da yake dai a makwanni biyu da suka gabata bayan fitowarsa daga asibiti an fara ganinsa a filin kwallo amma yana dogara sanda.

A cewar mai horar da tawagar kwallon kafar Fabio Mahseredjian ana samun gagarumin ci gaba a lafiyar dan wasan mai shekaru 26 wanda su ke kyautata zaton zai yi rawar gani a gasar cin kofin duniya ta bana da za ta gudana a Rasha.

Neymar din dai na cikin jerin ‘yan wasan da za su wakilci kasar a Rasha nan da kwanaki 22 masu zuwa, kuma ana fatan nan da 'yan kwanaki kalilan zai zanzare ta hanyar fara karbar atisaye kamar kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.