Wasanni

Neymar zai buga wasa karon farko cikin watanni 3

Neymar, yayin bugawa Brazil wasan sada zumunci da Japan a rana 10 ga watan Nuwamba, 2017.
Neymar, yayin bugawa Brazil wasan sada zumunci da Japan a rana 10 ga watan Nuwamba, 2017. REUTERS/Yves Herman

Neymar zai buga wasa na farko cikin watanni 3 bayan murmurewa daga jiyyar raunin da ya samu na karaya a kafarsa.

Talla

Mai horar da tawagar kwallon Brazil Tite ne ya bada tabbacin, inda ya ce, Neymar zai shigo fili ne a kashi na 2, na wasan sada zumuncin da Brazil zata fafata da Crotia yau Lahadi.

A ranar 25 ga watan Fabarairu da ya gabata, Neymar ya samu karaya a kafa, yayin wasa tsakanin kungiyarsa ta PSG da Marseille, a wasan gasar kasar Faransa ta Ligue 1.

Da fari an yi fargabar cewa dan wasan mai shekaru 26 ba zai samu damar bugawa kasarsa ta Brazil wasannin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha ba.

Sai dai bayan yi masa tiyata a Brazil dan wasan ya yi sa’a, inda ya ci gaba da samun sauki cikin sauri.

A kakar wasan da ta kare, Neymar ya ci wa kungiyarsa ta PSG kwallaye 28, a wasanni 30 da ya buga mata, kafin ya samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.