wasanni

Ajandar abubuwan da za su wakana a yau 4 ga watan 6 a bangaren kwallon kafa

Jugadores compiten en el videojuego FIFA18
Jugadores compiten en el videojuego FIFA18 Flickr-Gamescom EA Sports FIFA18

Wani lokaci a yau ne ake sa ran cimma wa'adin karshe na damar da aka bai wa kungiyoyin wasar kwallon kafa na Duniya su gabatar wa da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA jerin sunayen 'yan wasarsu da za su buga gasar wasar ta Duniya.

Talla

Bangaren kwallon kafa yau ake sa ran ta kasance wa’adin karshe na bayyana sunayen kungiyoyin wasar da za su kara da juna a gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya.

Bisa tsarin da aka yi dai ya zama wajibi tun kamin yau dukkanin kungiyoyin ‘yan wasar kasashen Duniya su gabatar da jerin sunayen ‘yan wasarsu 23 da za su buga wasar ga hukumar kwallon kafa ta Duniya wato FIFA.

Haka ma a wasannin share fagen shiga gasar ta Duniya da za’a yi, Morocco za ta buga da Slovakia, a yayin da Serbia za ta gwada tsawo da kasar Chile, kazalika Italiya za ta karbi bakuncin Netherlands ne a filin wasa na Torino.

Akwai kuma wasa tsakanin kasar Armenia da Moldova a yayin da aka soke wasa tsakanin kasar Malta da Moldova da aka shata yi wani lokaci a yau dinnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.