wasanni

Sakamakon wasannin sada zumunci na kasa da kasa

Wani mai tsaron gida a wasar kwallon kafa
Wani mai tsaron gida a wasar kwallon kafa

Yan wasar kasar Brazil Naymar da Firmino sun fidda kasar su kunya a wasar da suka buga da kasar Crotia da ci 2 da 1, wasar dai an buga ta ne a filin wasa na Liverpool da ke Ingila.

Talla

A sakamakon wasannin sada zumunci na kasa da kasa da aka gudanar inda a jiya Brazil ta lallasa Croatia da ci 2 – 0 a filin wasa na Liverpool da ke Ingila, ‘yan wasar Brazil Neymar da Firmino ne suka jefa kwallaye a ragar gidan Croatia.

Kasar Costa Rica kuma ta ci Northern Ireland 3 – 0 a wasar da suka buga a filin wasa na San Jose, inda suma ‘yan wasar ita kasar Costa Rica wato Venegas da Campbell da kuma Calvo suka zurara gwala-gwalai a ragar Northern Ireland.

Can a kasar Switzerland kuma a filin wasa na St Gallen, Peru ce ta lallasa takwararta wato Saudi Arebiya da ci 3 – 0, suma dai ‘yan wasar gidan kasar Peru wato Carrillo da Guerrero ne suka samu sa’ar saka gwala-gwalan a gidan ‘yan wasar kasar Saudi Arebiya.

A filin wasa na Vila-real da ke kasar Spain kuwa, Spain din da ta dauki bakuncin kasar Switzerland ne suka tashi wasa tsakanin su babu kare bin Damo, wato 1 – 1 kenan, ‘yan wasa guda biyu, Odriozola na bangaren Spain da Rodrigue na bangaren Switzerland ne suka saka kwallayen a ragar bangarorin guda biyu.

Akwai kuma wasar da za a buga tsakanin Spain da Switzerland a filin wasa na Vila-real da ke a kasar Spain, wani lokaci a yau dinnan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.